Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya ce ’yan Najeriya suna rayuwar ƙarya kafin gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur, matakin da ya ce ya zama dole don hana ƙasar rushewa.
Tinubu ya yi wannan bayani ne, yayin bikin yaye ɗaliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure (FUTA), in da ya samu wakilcin Farfesa Wahab Egbewole, Mataimakin Shugaban Jami’ar Ilorin, kamar yadda Aminiya ta rawaito.
“Tallafin, wanda aka tsara don taimakon talakawa, ya zama ya na cutar da su,” in ji shi.
“Rayuwar jin daɗin da muka ɗauka muna yi ba gaskiya ba ce domin ta na iya kai ƙasar nan ga rushewa.
“Cire tallafin man fetur da karya darajar Naira matakai ne masu wuya, amma wajibi ne domin ceto makomar ’ya’yanmu.”
Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Afirka ta Kudu daga Faransa.
NAHCON ta ce kowanne alhajin 2023 za a mayar masa da naira 60,080.
Shugaban ƙasar, ya kuma yi magana kan ficewa da matasan Najeriya ke yi zuwa ƙasashen waje, inda ya yi su daure su daina.
“Masana da ƙwararru da aka horar da su da dukiyar ƙasa suna barin ƙasa a lokacin da ake buƙatarsu fiye da kowane lokaci.
“Wannan ba ita ce mafita ba, ina tabbatar wa ’yan Najeriya cewa lokacin yin dariya na nan tafe, mun himmatu wajen gina Najeriya mai cike da inganci,” in ji shi.
Tun a ranar farko ta hawa mulkin shugaba Tinubu ne ya sanar da cire tallafin Man Fetur, wanda yasa man yin tashin Gwauron Zabo, in da ƴan ƙasar ke kokawa da tsadar rayuwa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Tsohon mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya Christian Chukwu ya rasu
-
EFCC ta gurfanar da wasu mutum biyu kan zargin damfara da sunan A’A Rano
-
APC ta rufe hedkwatarta da ke Abuja.
-
An hallaka mutum 1 wani kuma ya jikkata kan zargin satar kare a jihar Bauchi.
-
Ɗiyata “ta yi aiki wa Buhari shekaru huɗu a ofishin Osinbajo ba tare da ko kwabo ba-Buba Galadima