Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta mayar da yara sama da miliyan 1.5 makarantu a jihar.
Zulum ya ce adadin yara da aka mayar makarantu na wakiltar kashi 70 na yara miliyan 2.2 da aka gano ba sa zuwa makaranta a jihar.
Jami’ar Kwara ta rage wa masu buƙata ta musamman kuɗin karatu.
Malaman Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Kano sun tsunduma Yajin Aiki.
Bankin Duniya ya ce har yanzu Najeriya ba ta kama hanyar yaƙi da rashawa ba.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne ranar Talata, lokacin da ya ƙaddamar da makarantar Sakandaren Gwamnati ta Mairi, wanda Daraktan Bankin Duniya, Dokta Ndiame Diop, ya halarta.
Ya ƙara da cewa, cikin shekaru biyar da suka gabata, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen saka yara makaranta, inda ya bayyana cewa saura yara 700,000 za a mayar da su makaranta nan ba da jimawa ba.
Ya kuma bayyana cewa shirin ciyar da ɗalibai zai shafi yara 50,000, yayin da gwamnati ta raba kekuna 10,000 ga ɗalibai a yankunan karkara don rage musu wahalar zuwa makaranta.
Dangane da matasan da suka wuce shekarun makaranta, gwamnan ya ce gwamnati ta mayar da hankali kan ilimin fasaha da sana’o’i.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.