Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Wasu al’ummar Musulmai mabiya ɗariƙar Qadiriyya a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, sun daga tutar Mauludin Annabi Muhammad S A W, a hedkwatar ɗariƙar ta Afirka da ke birnin Kano.
Shugaban ɗariƙar Qadiriyya ta Afirka, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, ne ya jagoranci ɗaga tutar tare da ɗaruruwan mabiyansa.
Daman sun saba suna ɗaga tutar mai launin ruwan ganye, duk shekara a farkon watan Rabi’ul Auwal, watan da malaman Musulunci suka bayar da ƙarfi cewa a cikinsa ne aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad S A W, wanda miliyoyin Musulmai ke murnar haifuwarsa a faɗin duniya cikin watan.
Daga tutar dai a Najeriya tamkar wani sharar fage ne na fara gudanar da tarurrukan mauludi da al’umma ke shirya wa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kutu ta ɗaure likitan bogi da ya yi shekaru 10 ya na aiki a Abuja.
-
Tsadar Rayuwa: Ba Da Daɗewa Ba Abubuwa Za Su Yi Kyau -Gwamnatin Najeriya.
-
Ƴan Kasuwar Man Fetur Sun Fara Siyen Man Daga Matatar Dangote.
-
Ɗan Wasa Alex Song Mai Shekaru 36 Ya Jingine Takalmin Sa.
-
Ƴan Adawa Su Jira Zuwa Shekara Takwas, Muna Da Ƙwarin Gwiwa Ɗari Bisa Ɗari Abba Ne Zai Yi Nasara A Kotu,- Ahamd Abba Yusuf.