October 14, 2024

Musulman Najeriya Sun Daga Tutar Mauludin Annabi S A W.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wasu al’ummar Musulmai mabiya ɗariƙar Qadiriyya a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, sun daga tutar Mauludin Annabi Muhammad S A W, a hedkwatar ɗariƙar ta Afirka da ke birnin Kano.

Shugaban ɗariƙar Qadiriyya ta Afirka, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, ne ya jagoranci ɗaga tutar tare da ɗaruruwan mabiyansa.

Daman sun saba suna ɗaga tutar mai launin ruwan ganye, duk shekara a farkon watan Rabi’ul Auwal, watan da malaman Musulunci suka bayar da ƙarfi cewa a cikinsa ne aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad S A W, wanda miliyoyin Musulmai ke murnar haifuwarsa a faɗin duniya cikin watan.

Daga tutar dai a Najeriya tamkar wani sharar fage ne na fara gudanar da tarurrukan mauludi da al’umma ke shirya wa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *