June 27, 2022

Mutum 50 Sun Kamu Da Korona A Jihar Gombe.

Page Visited: 263
0 0
Read Time:59 Second

Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC, ta sanar da sabbin mutum 352 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya a ranar Juma`a 14 ga watan Junairun shekarar 2022.

NCDC ta ce, jihar Rivers ce kan gaba da mutum 119 sai jihar Lagos mai mutum 106 inda jihar Gombe ke na uku da mutum 50 babban birnin tarayyar Najeriya Abuja na da mutum 36 sai jihar Delta mai mutum 16 jihar Kaduna 14.

Sauran jihohin sune jihar Oyo 5 da jihar Taraba 5 a jiya Juma`a jihar Kano ce ta karshe da mutum guda.

Garba Shehu Da Wasu Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Najeriya Sun Kamu Da Korona.

Gwamnatin Bauchi Zata Karɓi Dubu Biyar Ga Duk Ɗalibin Da Yaƙi Karɓar Rigakafin Korona.

Korona Ta Ƙara Kama Mutum 2123 Ta Kuma Kashe 4.

Sanarwar da NCDC ta wallafa a shafinn na Tiwitter ta kuma ce zuwa yanzu mutum 250,361 suka tabbatar da cutar ta kama a Najeriya, inda kuma aka sallami mutum 223,495 da suka warke.

Zuwa yanzu dai tun daga bullar cutar Korona a Najeriya ta hallaka mutum 3,092 har lahira.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *