December 21, 2024

Mutum Sama Da 20 Sun Mutu A Wani Harin Da Sojoji Su Ka Kai Kasuwa A Sudan.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.

Wasu rahotanni na cewa harin rundunar sojin Sudan ya kashe mutane aƙalla 23 da kuma raunata wasu fiye da 40 a kudancin birnin Khartoum.

BBC ta rawaito, an kai harin ne a kan babban sansanin mayaƙan RSF a kudancin Khartoum, amma ya kuskure, in da ya faɗa a kan wata babbar kasuwa da ke kusa da gidajen mutane.

Ƙiyasin Majalisar Dinkin Duniya ya ce yaƙin da RSF ke yi da sojin Sudan a tsawon wata 18 ya yi sanadiyyar kisan mutane fiye da 150,000 da kuma raba wasu da dama.

Mutum 20 Sun Mutu 354 Sun Jikkata A Sudan Sakamakon Cutar Amai Da Gudawar Da Ta Barke.

Hezbollah Ta Fatattaki Sojojin Isra’ila A Ƙoƙarinsu Na Kutsawa Lebanon.

Ƙungiyar Hezbollah Ta Harba Rokoki Kan Runbun Jiyar Makaman Isra’ila A Tsakar Daren Jiya.

Rahotanni sun ce yawan waɗanda suka samu rauni ya zarce wanda asibitoci a yankin za su iya kula da su.

Tun daga ranar Juma’a faɗa ya ƙazance tsakanin RSF da sojin Sudan, a yankin da mayaƙan na RSF suke da ƙarfin iko sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *