Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci, NAFDAC, ta gargaɗi masu harkar sarrafa fulawa da su a faɗin ƙasar nan da su daina amfani da sinadarin zaƙi na sakarin (saccharin) da sinadarin buromet (bromate) mai sa fulawa ta tashi.
Darakta-janar ta hukumar, Mojisola Adeyeye, ce ta yi wannan gargadi a lokacin da take ganawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN).
Ta kuma ba da tabbacin cewa duk gidan biredin da aka samu da amfani da waɗannan sinadarai zai fuskanci hukunci kuma za su yi amfani da tsarin bindiddigi na kayan abinci da aka sarrafa wajen gano masu kunnen ƙashi
“Mukan fita waje domin gane wa idanunmu, kuma yawanci mukan samu ƙorafi ne ga wasu al’umma.”
“Mun rufe gidajen sarrafa fulawa da dama saboda amfani da sinadarin buromet wajen yin biredinsu”.
Ta ce idan suka gano ko wani ya ɗanɗana kuma ya shigar da rahoto to lallai za su tabbata sun sun rufe gidan biredin.
Hakazalika ta ce akwai gidajen ruwa da suka rufe saboda rashin samar da ruwa mai inganci ko marar kyau.
“Sashen Bindiddiginmu na da muhimmanci domin ta da shi ne muke tabbatar da cewa abin da aka kawo mana muka gwada ingancinsa, shi ne wanda ake sayarwa a kasuwa.”
“idan muka yi bincike mukan tabbatar da mun taho da samfuri domin gwadawa a ɗakin gwaje-gwajenmu inda mukan gani gaskiyar abin da ke ƙunshe a cikin wannan abin.”
Ta ce a wasu lokutan bayan mutane sun yi rajista sukan koma su fara canja tsarin yadda suke samar da abu.
“wannan ne abin da muke kira da bindiddigin kasuwa,” ta faɗa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.
-
Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.
-
Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.
-
Sarakunan da Fintiri ya naɗa bayan ƙirƙirar masarautu 7 a jihar Adamawa.