January 22, 2025

Najeriya Ta Fi Samun Tsaro A Mulkin Tinubu -Nuhu Ribadu.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Mai bai wa shugaban ƙasar Najeriya shawara kan sha’anin tsaro Mallam Nuhu Ribadu, ya bigi ƙirji cewa ƙasar ta fi samun ingantuwar tsaro a mulkin shugaba Tinubu idan aka kwatanta da zamanin gwamnatin da ta gabace su.

TRT ta rawaito, Ribadu na cewa “Ina tabbatar muku cewa a yau Abuja ta na cikin tsaro; a yau kuna iya tafiya da ƙafa ko tuki da daddare daga Abuja zuwa Kaduna ko Lokoja ko Minna ko Lafiya cikin aminci.”

Biyan kudin fansa ba ya hana ƴan bindiga kashe wanda aka yi garkuwa da shi – Gwamna Radda.

Sojojin Nijar Sun Kashe Ƴan Bindiga 60

Sojin Saman Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga A Dazukan Kaduna Da Zamfara.

Mallam Nuhu, ya kuma ce a halin yanzu mutum zai zama ya yin tuku zuwa ko’ina a fadin ƙasar ba tare da tsoro ba, a cikin mulkin su na shekara ɗaya da wata uku “ba ka isa ka yi haka ba a shekarar 2022” in ji shi.

Arewa masu Yammacin Najeriya da wasu sassan ƙasar na fama da rashin tsaro tun kafin kafuwar gwamantin Tinubu, wanda ya ci gaba da ɗore wa har bayan kafa gwamnati a shawarar 2023, in da wasu na ganin matsalar na ƙara ƙamari duk da iƙrarin da gwamnatin ke yawan yi na samu nasarar kan ƴan ta’adda da ƴan bindiga da ke garkuwa da mutane gami da ƙarshe su da sace dukiyoyi su.

Ko a baya-baya nan sai da masu garkuwa suka kashe Sarki Gobir na garin Gatawa da ke jihar Sokoto, wani abu da ba sa ba gani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *