April 5, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Nan da Makwanni Ƴan Najeriya za su yi murmushi a 2025 – Shettima.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya ce ƴan Najeriya za su yi murmushi kuma za su ci gaba a shekarar 2025, ganin yadda tattalin arzikin kasar ke kan hanyar bunƙasa.

Daily Trust ta rawaito, Kashim ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan wata ziyara da ya kai wa shugaba Bola Tinubu a Legas ranar Laraba.

“Tattalin arzikin ƙasar ya fara tashi, kuma nan da makonni da watanni masu zuwa ƴan Najeriya za su fara murmushi.

“Muna aiki tare da Majalisar Dokoki ta ƙasa don samar da ingantattun hanyoyin magance ƙalubalen da muke fuskanta na kasa.

“Babu wata al’ummar da ta tsira daga guguwar tattalin arziki a fadin duniya, in ji Kashim.

EFCC ta kama makusanciyar tsohon Gwamnan Delta Okowa kan badaƙalar Tiriliyan 1.3

Kwastam za ta ɗauki sabbin ma’aikata 3,927 a Najeriya.

Matatar Dangote haɗin gwiwa da kamfanin mai na MRS za su sayar da fetur a kan N935 duk lita.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce “tikicin da ke faruwa a Ukraine da sauran al’amuran duniya da dama su na yi mana illa saboda muna cikin al’ummar duniya.”

Sai dai ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa ƙasar ta na kan hanyar samun ci gaba mai dorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *