Daga Sani Ibrahim Maitaya
A cikin wata fitowar ban mamaki da ke cike da barkwanci da juriya, Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta rubuta wata wasika mai zafi da ta kira da “wasikar neman afuwa” wacce ta aike wa Shugaban Majalisar Dattijai Godswill Akpabio, tana sukar abin da ta bayyana a matsayin al’adar jin daɗi da biyayya da ke cikin zaurukkan majalisun kasa.
A cikin wasikar wadda ke dauke da yawan barkwanci da kwaikwayo na nadama, Sanata Uduaghan tana “neman afuwa” bisa “babban laifi” na ci gaba da rike mutuncinta da girmama kanta, duk da wasu bukatu da ta yi ishara da su a matsayin marasa dacewa daga shugaban Majalisar.
“Na yi nazari sosai kan gazawata ta rashin gane cewa nasarar aiki a wasu bangarori ba ta samuwa ta hanyar cancanta ba, sai dai ta hanyar tsohuwar dabi’ar biyayya — wacce ke da matukar sirri,” in ji ta.
Sanata Uduaghan ta soki abin da ake kallon sa a matsayin tsammanin cewa ‘yan majalisa mata dole su fifita biyayya ta kai da kai a kan kwarewa, da amincewa a sirrance a kan hidimar jama’a. Ta koka kan “mummunan sakamako” da rashin yarda da irin wadannan bukatu ya haifar — ciki har da jinkiri wajen wuce dokoki da raunata girmama kai.
A wani bangare a cikin wasikar, ta yi ba’a da cewa: “Don Allah ku nemi waje a cikin zuciyar ku mai girma — wacce aka boye a karkashin yawan jin kai — ku yafe wa wannan mace mai kai da kai, wacce ta yi kuskuren tunanin cewa kujerar ta a Majalisar Dattijai ta samu ta hanyar zabe, ba ta hanyar wata irin biyayya ba.”
Sanata Uduaghan ta kammala wannan wasikar barkwanci da tabbatar da kudurin ta na ci gaba da kasancewa “Maras Tsoro, Maras Siyan Kai, Kuma Maras Rushewa,” tana mai aika sako a sarari cewa ba za ta lamunce duk wani matsin lamba ba.
Tun bayan fitowar wannan wasika, ta tayar da gagarumar mahawara a cikin siyasar Najeriya da kungiyoyin fararen hula, inda ake tattauna batutuwa kan jinsi, tsarin iko, da mutunci a cikin shugabancin kasa.