March 12, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

NITDA ta gargaɗi masu kafafen internet da ke kan WordPress.

Hukumar Bunkasa Fasahar Bayanai ta kasa (NITDA) ta gargadi masu gidajen yanar gizo kan wata babbar matsalar tsaro a cikin plugin Jupiter X Core na WordPress, wanda zai iya bai wa masu kai farmaki damar karɓar cikakken ikon sarrafa shafukan da abun ya shafa.

Wannan bayani ya fito ne a wata sanarwa da tawagar Shirye-shiryen Gaggawa da Mayar da Martani Kan Matsalolin Kwamfuta ta hukumar ta fitar a ranar Laraba.

Matsalar tsaron, wadda aka gano mai lamba CVE-2025-0366, wata gagarumar nakasa ce ta samun iko ba tare da izini ba, wadda ka iya bai wa masu hari damar aiwatar da lambar barnata ko samun ikon gudanarwa ba tare da wata tantancewa ba, a cewar NITDA.

“Haka kuma, idan aka yi amfani da wannan masu hari na iya canza abun ciki, saka cutar kwamfuta, ko ɓata fuskar shafukan yanar gizo, wanda ke da barazana ga shafukan da ke kula da bayanan sirrin masu amfani,” in ji hukumar.

Masu gidajen yanar gizo da ke amfani da wannan plugi ɗin na da buƙatar sabunta shi zuwa sabon sigar da aka gyara, wato sigar 4.8.8, tare da cire duk wasu plugin da ba a amfani da su ko tsofaffi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *