April 1, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

NNPP ta nesanta ta da Kwankwasiyya da su ƙungiyoyi ta na mai gargadin su dena bayyana kansu a matsayin cikakkun ƴaƴan jam’iyyar.

Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta nesanta kanta daga ƙungiyoyin Kwankwasiyya da The National Movement (TNM), ta na gargadin su da su daina bayyana kansu a matsayin bangare na zama cikakkun membobi da shugabancin jam’iyyar NNPP.

A wata wasika da jam’iyyar ta fitar a ranar 20 ga watan Maris 2025, wacce aka bai wa manema labarai, NNPP ta tunatar da ƙungiyoyin bukatar ci gaba da kiyaye matsayar da ke cikin yarjejeniyar fahimta juna (MoU) da aka kulla da su, wacce ta kare tun shekarar 2023.

A cikin wasikar, NNPP ta jaddada cewa shugabannin ƙungiyoyin Sanata Rabiu Kwankwaso da Dattijo Buba Galadima dole ne su mutunta kawo ƙarshen yarjejeniyar, da aka kulla da jam’iyyar a lokacin shirin babban zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

An kuma aika kwafin wasikar ga Sufeto Janar na Ƴan Sanda da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Wasikar tana dauke da sa hannun Wanda ya kafa jam’iyyar kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na jam’iyyar NNPP Dakta Boniface Aniebonam, da kuma Shugaban ta na Kasa Dakta Agbo Major.

Idan za’a iya tunawa jam’iyyar NNPP ta kulla yarjejeniya da Ƙungiyar Kwankwasiyya da Kwankwaso ke jagoranta da kuma TNM ƙarƙashin jagorancin Buba Galadima, domin amfani da dandalin jam’iyyar a matsayin wata kafa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023, in da Kwankwaso ya kasance ɗan takarar jam’iyyar.

An tsara cewa yarjejeniyar za ta kare bayan zaɓen, amma bayan jam’iyyar ta rubuta wa ƙungiyoyin wasiƙa a watan Yuli 2023 tabna sanar da su kawo ƙarshen yarjejeniyar, hakan ya jawo ce-ce-ku-ce daga bangaren ƙungiyoyin.

Biyo bayan soke yarjejeniyar, ƙungiyoyin sun ki mutunta hakan kuma suka ci gaba da nuna kansu a matsayin membobin jam’iyyar, wanda ya haifar da korar wasu daga cikin su saboda aikata laifukan sabawa jam’iyya.

A wasiƙar, jam’iyyar NNPP ta ce “Da fatan za ku koma ga wasiƙar mu ta 28/7/2023, in da muka sanar da ku cewa NNPP ta janye daga yarjejeniyar fahimtar juna da muka kulla da ku, Ƙungiyar Kwankwasiyya da NNPP.

“Amma har yanzu mun lura cewa kuna ci gaba da bayyana kanku a matsayin cikakkun membobi da shugabannin NNPP.

“Dole ne ku dakatar da wannan dabara ta zamba da ƙoƙarin ruguza jam’iyya, domin tun daga ranar 28 ga watan Yuli 2023, tsarin shugabanci da jagorancin NNPP ya koma hannun waɗanda suka kafa jam’iyyar da shugabannin ta na asali.

“An shawarce ku da ku bi shawara yadda ya kamata, kuma ku daina yaudarar al’umma” inji bayanin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *