October 16, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

NNPP Ta Umarci Masu Son Yi Takara A Jam’iyyar Su Ajiye Muƙamansu.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

A jihar Kano da ke Najeriya, jam’iyyar NNPP, ta yi kira ga dukkanin masu sha’awar tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma ko kansila, ƙarƙashin tutar jam’iyyar da su yi gaggawar ajiye mukaman da suke riƙe da su na gwamnati nan take ko kuma kafin ƙarshen watan nan na Agustan 2024.

Kafafen yaɗa labarai a jihar Kano, sun rawaito cewa, shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano Dr. Hashim Suleiman Dungurawa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai daya gudana a birnin Kano domin bayyana matsayar jam’iyyar dangane da dokar hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano KANSIEC.

Za a yi zaɓen ƙananan hukumomin jihar ne a watan Nuwamba, in da hukumar zaben jihar ta ce za ta yi gwajin shan kwaya ga masu sha’awar tsaya wa takarar shugabancin ƙaramar hukuma ko kansila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *