January 15, 2025

PDP ta sha alwashin kwace mulkin Najeriya a hannun APC.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Jam’iyyar a Najeriya ta PDP ta ce za su samu ƙarin gwamnoni a zaɓen 2027, ƙari a kan guda 12 da take da su a yanzu, sannan za ta karɓe mulkin ƙasar.

BBC ta rawaito, jagororin jam’iyyar ne suka bayyaka haka a lokacin da su ka kai ziyara ga Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, kamar yadda tashar.

Ma’ajin jam’iyyar, Alhaji Ahmed Yayare ne bayyana hakan a madadin jam’iyyar, inda ya ce yanayin yadda ƙasar ke fama da taɓarɓarewar tattalin arziki ne ya sa PDP za ta samu sauƙin samun nasara a 2027.

Amnesty Ta Nemi A Saki Ɗan PDPin Da Ke Tsare A Sokoto Kan Wallafa Bidiyon Gwamna Da Matarsa.

Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.

Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.

Ya ƙara da cewa, “babu abin da zai hana PDP karɓe mulkin ƙasar. Yanzu APC ba ta abin da za ta yi kamfe da shi saboda yunwa da talauci ya yi a ƙasar. Idan suka fita kamfe sai an jefe su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *