Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour ya yaba wa rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, bisa janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi.
Obi ya ce wannan gayyata ba ta da muhimmanci, kuma tana iya ƙara dagula lamarin da tuni ya riga ya yi tsami.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an gayyaci Sarkin ne tun da farko, bisa zargin kisan kai da aka ce ya faru yayin bikin Sallah a ranar Lahadi a jahar, bayan da aka fitar da gargadi kan gudanar da hawan Durbar.
Hawan Durbar wata al’ada ce da ake gudanarwa bayan sallar Idi a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan Sanusi ya dawo daga sallar Idi, inda ya tafi da ƙafa, amma ya koma fada bisa doki.
Sai dai bayan korafe-korafe daga jama’a game gayyatar, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun, ya janye gayyatar da aka aikawa Sanusi.
Egbetokun ya umurci rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano da su karɓi bayanin Sanusi dangane da lamarin.
A cikin martanin sa tsohon gwamnan jihar Anambra, a wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na X ranar Litinin, ya yaba da matakin janye gayyatar.
Ya ce “Ina so in yaba wa Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya bisa wannan mataki na hikima da suka ɗauka na janye gayyatar da suka aikawa Mai Martaba Muhammadu Sanusi II. A dai-dai wannan lokaci da ake cikin matsin lamba a cikin al’umma, wannan gayyata ba ta da muhimmanci kuma tana iya ƙara dagula al’amurra.
“Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano na aiki yadda ya kamata, kuma tana da ƙwarewar da ake bukata don warware irin waɗannan matsaloli a cikin jihar. Wannan shine dalilin da ya sa muke da manyan jami’ai kamar Kwamishinonin ‘Yan Sanda da Mataimakan Sufeto Janar (AIGs) a matakin jihohi da na shiyya.
“ina ƙara jaddada godiya ta kan janye gayyatar” In ji Peter Obi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya