Rashin Ƙarfafawa Ke Durƙusar Da Masu Fasahar Mu A Najeriya Musamman Ƴan Arewa.

Page Visited: 138
0 0
Read Time:3 Minute, 10 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Allah ya azurta ƴan Arewa da mutane iri-iri da suke da baiwar ƙirƙire-ƙirƙire da ƙere-ƙere da yawan gaske kuma a kowane sako da lungu na ƙasar nan musamman ma a wannan yanki namu na Arewa, to amma basa samun cigaba.

Suna rasa cigaba ne saboda rashin ƙarfafawa daga gwamnatoci, mawadata da sauran al’ummar unguwa ko yankin da suke.

Ba wai ina nufin idan yaro ya taso yana ƙera wani abu a ɗauki kuɗi a bashi ba, abinda nake nufi shine a sayi kayansa tanan ne zai samu kwarin gwiwar cigaba da inganta abinda yake ƙerawa saboda ya fahimci ana so, don haka dole zai yi amfani da ribar da yake samu domin ya sayo kayan aiki.

Ko kuma gwamnati ta dinga ɗaukar su tana kaisu suna yin ƙwasa-ƙwasai kan fasahar ta su, wannan zai taimaka musu sosai, amma wata matsala ita ce yin rijista da hukumomin da suka dace, wanda da yawa wajen yin rijistar ana samun matsala ta rashin kuɗi, wanda rashin rijistar yana hana musu cigaba, anan abinda gwamnati ya kamata sai ta basu bashin wasu kuɗaɗe domin ta haka ne za su iya yin rijista da hukumomi ta yadda za su iya yin mu’amalar kasuwanci da kowa.

A baya nayi maganar sayen kayan su, gaskiya a wannan fannin akwai matsala sosai, kaɗai babbar hanyar taimako ita ce sayen kayan masu fasaha.

To amma ko a labarai ni ban taɓa ganin cewa gwamnatin tarayya ko ta jihohin da ake samun irin haka sun sayi kayansu ba.

Musamman idan muka kalli ƙera motoci masu amfani da hasken rana da da babura masu ƙafa uku da Mustapha Gajibo ya yi a jihar Borno, wannan kaɗai zai kawo rage barazanar gurɓatar yanayi da duniya ke ta ƙoƙarin kawo karshen sa.

A mafiya yawan jihohin mu, ai akwai matsala sufuri, wanda ya kamata gwamnatoci su sayi kayan su, kamar misali sai gwamnati ta saya ta kai makarantu domin a dinga ɗiban ɗalibai da malamai, hakan ma zai kawo sauki.

Ya kuke gani idan gwamnatin jihar Borno ta sayi motocin nan kamar guda 100 a gun Mustafa Gajibo an taltalin arzikinsa zai bunƙasa zai ƙara samun dama ya ɗibi matasa aikin yi, kunga an ragewa gwamnati nauyi.

Haka shima matashin da ya ƙera babur mai kafa uku a jihar Kano, da sauran masu ƙere-ƙere da muke dasu a sassan Arewacin Najeriya.

Nayi maganar rashin taimaka musu tabbas akwai wannan matsalar na zanta da mutane da dama masu irin waɗannan fasahohi amma abinda suke kokawa da shi kenan.

Wani abokina a wata jiha da ke nan Arewacin Najeriya ya bani labarin cewa, abokin sa shine mai ɗaukar hoton matar wani gwamna mai ci a halin yanzu, lokacin bikin ɗan su, wani mai ɗaukar hoto ɗan jihar Legas aka ke aka ɗauko, ya je ya ɗauki hoton da ake cewa Pre-wadding picture wanda bai taso daga jihar sa ta Legas zuwa nan Arewa jihar da ya yi aikin ba, sai da aka saka masa kuɗi Naira miliyan 7 sannan ya taso, kuma bayan zuwan sa aka yi ta ɗauwainiya da shi har ya yi kwana uku ya koma jiharsa, kawai a aikin kwana uku na Pre-wadding picture ya ci miliyan 7 ya koma a bin sa.

Shi kuma wanda ya saba ɗaukar musu hoto da daɗi babu daɗi shine ya yi aikin biki da abokansa da ya gayyato suka taya shi aiki, ku duba wahalar aikin biki duk aka yi aka gama, Naira dubu 100 aka bashi, ku faɗan wannan taimakon ɗan Arewa a kai ko kuma ƙarya shi?

Kunga ɗan Arewa ya tsallake nasa ya ɗauko bare ya taimake shi, kuma fa ba wai yafi ɗan Arewan kwarewa bane.

Gaskiya akwai matsala yakama manyan Arewa masu hali da kowa da kowa mu farka mu taimaki junan mu.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ra'ayi

Anya Kuwa Kasan Wani Tela Da Ke Ɗinka Ɗan Kamfai A Najeriya Duk Da Irin Mahimmancinsa.

  Yayin da wasu ƴan Najeriya ke kokawa da matsin taltalin arziki ake kuma nemo hanyar kawo karshensa wani mai amfani da kafafen sada zumunta Abdulwahab Said Ahmad na da ra’ayin cewa matuƙar ba a rungumi ƙananan ƙere-ƙere a gida ba to ba za a taɓa samun sauyi ba. “Ba zamu fita daga cikin halin […]

Read More
Ra'ayi

Fetur A Arewa: Bauchi Na Maraba Da Buhari- Dr Aliyu Tilde.

Kaddara Bauchi da Gombe dai kaddara ta rubuta kasancewarsu tare har abada. Farko, a Daular Usumaniya lokacin da Yakubun Bauchi da Buba Yero suka assasa masaurautunsu, an samu rashin jituwa tsakaninsu a kan ina ne iyakar kowannensu. Bayan da aka yi wani yaki a tsakaninsu har ya kai ga kashe juna, sai Muhammadu Bello a […]

Read More
Ra'ayi

Me Ya Sa Aurenmu Ya Ke Yawan Mutuwa?

Mun dan yi wani bincike da mu ka gano wasu abubuwan da ke saurin kashe aure ko da maaurata suna son junansu, za mu fara dauko su daya bayan daya muna tattaunawa. Abu na farko da ke cikin wannan rukunan da ke kawo matsaloli a zamantakewar auranmu (hausawa) har ya kai ga rabuwa shine rashin […]

Read More