Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin gamsuwa kan yadda gwamnatin tarayya ta bada aikin rabon tallafin shinkafa da kuma batun tafiyar da tsaro a jihar Kano.
A wani sako da ya wallafa a shafin X, Kwankwaso ya bayyana damuwa kan yadda aka bai wa Gwamnonin jihohi 35 shinkafar don rabawa al’umma amma jihar Kano aka mika ta a hannun ‘yan jam’iyyar APC, abinda ya bayyana da cewa siyasa ce zallar ta.
“Wannan cin zarafi ne ga tsarin dimokuradiyya”, inji Kwankwaso.
“Ku tabbatar cewa ba a sake kawo taliya mutane sun karɓa ba”-Kwankwaso.
DSS Sun Cafke Shugaban NLC Joe Ajaero.
Biyan kudin fansa ba ya hana ƴan bindiga kashe wanda aka yi garkuwa da shi – Gwamna Radda.
Ya yi kira ga shugaban kasa Tinubu ya gaggauta dakatar da abinda ya kira ga “yiwa dimokuradiyya zagon kasa”
Haka kuma, Kwankwaso ya koka kan yadda aka sauye shugabannin hukumar tsaro ta farin kaya a Kano cikin mako biyu.
Kwankwaso, ya ce hakan zai iya yin illa ga tsaron jihar.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.