Gwamnan jihar Bauchi Sen. Bala Abdulkadir Mohammed, ya miƙa sakon ta’aziyarsa bisa rasuwar Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi Bauchi.
Gwamna Bala cikin sakon daya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna alhini bisa rasuwar malamin.
Yace “Cikin alhini tare da fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki, mun wayi gari da rasuwar ɗaya daga cikin malaman addinin Musulunci daga nan jihar Bauchi, Sheik Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, bayan fama da jinya.”
“Yayin da muke roƙa masa gafarar Allah maɗaukakin Sarki, a madadin ni kaina, iyali gwamnati da ɗaukacin al’ummar Bauchi, ina isar da ta’aziyya ga iyalan marigayi Malam da almajiran sa. Allah ya ba mu haƙurin juriya, ya haskaka kabarin sa.” Cewar Gwamnan Bala.
Gwamnan yayi addu’ar Idan ajali ya riske mu, ya Allah ka sa mu cika da imani, Amin.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP
-
Babu wani gurbi a gidan gwamnatin Delta cewar Dennis Guwor ga ƴan takarar gwamnan jihar.