Rikicin Siyasa Na Kara Yin Zafi A Jam`Iyyar NNPP Yayin Da Kwankwasiyya Ke Rasa Jiga-Jigai.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

A yan kwanakin nan rikicin cikin gida a jam`iyyar NNPP a jihar Kano na ƙara ɗaukar sabon salo tun bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar, ta yi zaɓen ƙananan hukumomi, daman kafin nan batun fitar ƴan takarara ne ya fara bayyana irin tarin rikicin da jam’iyyar ke fama da shi.

Jagoran jam`iyyar Sanata Rabi`U Musa Kwankwaso, ya jagoranci canza wa jam`iyyar tambari daga mai kayan marmari zuwa tambarin kayan rubutu, canjin tambarin da ya kai ga zuwa kotu, bayan da wani bangre da su ka ce su ne asalin yan jam`iyyar su ka shigar da ƙara suna masu ƙorafin Kwankwaso ya kwace jam’iyyar daga hannun wanda ya kafa ta wato Dokta Boniface Okechukwu Aniebonam.

A wani hukunci na baya-bayan nan da wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a jihar Abia, karkashin Jagorancin mai sharia Hon. Justice C.U. Okoroafor, ta yi ta ba da umarnin karɓe shugabancin jam’iyyar NNPP daga hannun Rabiu Musa Kwankwaso nan take ta kuma maida wa wanda ya kafa jam’iyyar, Dokta Boniface Okechukwu Aniebonam.

Ko a jihar Kano wani ɓangare na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Barrister Ɗalhatu Usman Shehu ya ce sune ƴan jam’iyyar kuma Ɗalhatu ne shuganan jam’iyyar ta jihar Kano ɓangaren mai kayan marmari, in da kuma Dr. Hashim Suleiman Dungurawa ke shugabanta jam’iyyar ɓangaren mai littafi.

Rikicin na ƙara ruruwa in da wata ƙungiya ta bulla mai suna “Abba Tsaya Da Ƙafarka” kuma ta ci gaba da ribatar ƴaƴan jam’iyyar NNPP, wanda suke son gwamnan ya dena karɓar umarni daga mai gidansa Rabi’u Musa Kwankwaso.

Wannan dai a iya cewa shine ke tinzira wutar rikicin, ƙungiyar Kwankwasiyya ta fara yin asarar wasu jiga-jiganta in da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar kamarar hukumar Dala Aliyu Sani Madaki ya fice daga ƙungiyar ya na mai cewa ƙarya ce kuma yaudara ce gami da cin amana, to amma har yanzu bai fice daga jam’iyyar ta NNPP ba kuma bai bayyana ka yana ɓangaren mai kayan gwari bane ko kuma mai littafi ba.

Shi kuwa a nasa bangaren ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, Alhassan Rurum ya ce shima ya bar tsarin na Kwankwasiyya kuma yana nan a jam’iyyar NNPP amma bangaren mai kayan marmari, ya na mai cewa ya bi umarnin kotu.

Ana cikin wannan ne wani rahoto da jaridar internet ta Daily Nigerian ta fitar ya ce, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ki halartar wasu tarruka na Kwankwaso ta re da ƙin ɗaga wayar sa, abin da Martaba FM Online bai kai ga tabbatar wa ba,

Jaridar ta ce wasu majiyoyi sun tabbatar mata datuni Abba ya fara amsa kira bayan da “aka nusar da shi cewa Kwankwaso ne ke juya gwamnatin sa in da kusan kashi 90 na mukaman da Abba ya yi daga ɓangaren Kwankwaso ne.”

Majiyoyi sun baiyana cewa Abba ba ya jin daɗin “ƙarfa-ƙarfa” da Kwankwaso ya ke yi masa inda ya ya fara nuna alamun boyewa masu kira da ya tsaya da kafar sa domin ci gaban sa na siyasa da ma jihar Kano baki ɗaya.

Tun lokacin da aka ga gwamnan a bikin murnar zagayowar haihuwar Kwankwaso, har yanzu basu sake haduwa ba, in ji jaridar.

Majiyoyin sun kara da cewa har Abuja Kwankwaso ya bi gwamnan amma Abba bai bari sun hadu ba, kuma har dan aike ya tura amma Abban ya ki ganuwa a wajen Kwankwaso.

Sai dai Daily Nigerian ta gaza jin ya bakin Kwankwaso, amma wani na jikin sa ya nuna rashin jin dadin halaiyar da Abba ke nunawa Kwankwason.

Shi ma mai magana da yaqin Abba, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya ki cewa uffan akan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Proudly powered by WordPress | Theme : News Elementor by BlazeThemes