January 31, 2023

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Ta Gargadi Mazauna Jihar Kan Atisayen Harbin Bindiga A Kalebawa.

Page Visited: 66
0 0
Read Time:41 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

A yau Alhamis rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano a Arewa maso Yammacin ƙasar nan za ta gudanar da atisayen harbin bindiga a hawan Kalebawa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa tin daga ƙarfe shidan wannan safiya zuwa shidan yammaci.

Rundunar ta ja hankalin al’ummar jihar musamman mazauna yankin da atisayen zai gudana cewa kar su tsora.

Cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakinta Sifiritandan Ƴan Sanda Abdullahi Haruna Kiyawa ta shawarci mazauna yankin su ne sanci gun atisayen “mazauna wannan yanki musamman Kauyukan Dambazau, Gangaren Dutse, Tumfafi, Kakurum, da Dandalama da kuma sauran garuruwan da suke makotaka da su, kauracewa wannan wuri, kuma kada su firgita da karar Harbin da zasu rinka ji yayin wannan Atisaye har sai an kammala.”

Bisa al’ada rundunar ta saba ta kan gudanar da atisayen lokaci bayan lokaci.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *