Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Rundunar Ƴan sandan Najeriya ta ƙaryata rahoton bazuwar ƴan ta’adda a Lugbe da ke Abuja. - Martaba FM Rundunar Ƴan sandan Najeriya ta ƙaryata rahoton bazuwar ƴan ta’adda a Lugbe da ke Abuja. - Martaba FM

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta karyata ikirarin da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa, akwai ‘yan ta’adda guda 79 a yankin Lugbe na Abuja, tana bayyana rahoton a matsayin karya da yaudara.

A yayin da damuwa kan tsaro ke karuwa a Babban Birnin Tarayya, ‘yan sanda sun tabbatar wa mazauna birnin cewa babu wani bayani na sirri da ke tabbatar da hakan.

A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Mai Magana da Yawun Rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya musanta sakon da ya bazu a WhatsApp da sauran dandamalin sadarwa, yana mai cewa hakan yunkuri ne na tayar da hankulla da haddasa rudani a birnin.

Rundunar ‘Yan sandan ta kara da cewa binciken sirri da rahotannin tsaro sun tabbatar da cewa, babu wani nau’in ayukkan ‘yan ta’adda a Lugbe ko kewayen ta.

Rundunar ‘Yan sandan ta bukaci ‘yan Najeriya da su dogara kawai da bayanai daga hanyoyin hukuma, ciki har da shafukan sada zumunta na rundunar, tare da gargadin mutane kan yada labaran tsaro marasa tushe da ka iya haddasa firgici.

Ya ce “Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron dukkanin mazauna babban birnin tarayyar da kasa baki daya.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *