Kwamishinan Ƴansanda na Jihar Kebbi CP Bello Sani, a ranar Laraba ya mikawa iyalan marigayan jami’an ƴansanda 23 takardun karɓar kuɗi da suka kai naira miliyan miliyan arba’in da shida, da dubu dari shida da saba’in da biyu, da dari tara da tas’in da da biyu.
Wannan tallafi na kudi an bayar da shi ne a ƙarƙashin shirin Group Life Assurance, da IGP Family Welfare, da Group Personal Accident Schemes, kuma an mika shi ne a madadin Sufeto Janar na Ƴansanda Kayode Egbetokun.
Mataimakin Kwamishinan Ƴansanda mai kula da Harkokin Gudanarwa DCP Aminu Babale, shine ya miƙa chekin ga iyalan mamatan a wani biki mai cike da alhini da aka gudanar a Hedkwatar ‘Yansanda ta Jihar da ke Birnin Kebbi.
Yayin da yake jawabi ga waɗanda suka amfana, Babale ya ce, “Ina rokon ku da ku yi amfani da wadannan kuɗaɗe yadda ya kamata, domin magance matsalolin ku na gaggawa da kuma saka jari a goben iyalan ku, musamman ta fuskar ilimi da daidaita tattalin arziki.”
Baya ga bayar da tallafin kudin, taron ya kasance wata dama ta tunawa tare da yin addu’o’i ga jami’an da suka rasa rayukan su yayin aiki.
Muhammad Sani wanda ya yi magana a madadin waɗanda suka amfana, ya bayyana matukar godiyar sa ga Sufeto Janar, da CP Sani, da Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kebbi.
Ya yaba da wannan karamci da goyon baya da aka nuna musu a wannan mawuyacin lokaci, tare da yin addu’a domin samun ƙarfi, hikima, da cigaban shugabannin Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.