Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Rundunar sojin saman Najeriya ta sha alwashin ci gaba da kare rayukan al'umma jihar Zamfara. - Martaba FM Rundunar sojin saman Najeriya ta sha alwashin ci gaba da kare rayukan al'umma jihar Zamfara. - Martaba FM

Daga Sani Ibrahim Maitaya

Shugaban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya ziyarci Gusau babban birnin Jihar Zamfara, don wata ziyarar aiki ta yini guda a Hedikwatar Rundunar 207 ta Sojojin Saman Najeriya dake Gusau.

Wannan shi ne karo na farko da Air Marshal Abubakar ya ziyarci jihar Zamfara a hukumance, tun bayan nada shi a matsayin Shugaban Hafsan Sojin Sama.

Da isarsa manyan jami’an soja ne suka tarbe shi, ciki har da Kwamandan Atisayen Operation Fansan Yamma Manjo Janar Oluyinka Soyele.

Daga nan sai ya wuce don duba rundunar sojojin Runduna ta 207 suka kafa don gaisuwar ban girma.

Da ya ke gana wa da manema labarai bayan ya ziyarci gwamnan jihar Daula Lawal shugaban sojin saman ya ce, sun ziyarci jihar Zamfara ne, domin jajanta wa da bayar da haƙuri ga ƴan ba ruwa na da harin soja ya rutsa da su bisa kuskure, ya na mai cewa rundunar ta yi bincike tabbbatar an kashe farar hula ne bisa kuskure, kuma hakan ta faru ne a ƙoƙarin kare rayuwar su daga ƴan binga.

Ya kuma sha alwashin ci gaba da ƙare rayuka da dokiyoyin al’ummar jihar.

Shima gwamnan jihar ya ce, za su ci gaba da haɗa kai da sojojin domin ci gaba da yaƙar ƴan bindiga da suka hana zaman lafiya, ya na mai tabbatar da an kai hari kan farar hula ne bisa kuskure.

Air Marshal Abubakar ya samu rakkiyar manyan jami’an soja daga sassa daban-daban na rundunar sojin sama.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *