December 21, 2024

Sallamar da Gwamna Abba ya yi wa Sakataren Gwamnati da Kwamishinoninsa 5.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da gyare-gyare a majalisar zartarwar jihar, inda ya cire wasu, sannan ya sauya wa wasu ma’aikatu.

hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya soke ofishin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, wanda Alhaji Shehu Wada Sagagi ke riƙewa, sannan ya cire sakataren gwamnatin jihar, Dokta Baffa Bichi saboda rashin lafiya.

Sanarwar ta Kuma ce gwamnan ya cire kwamishinoni guda biyar: Ibrahim Jibril Fagge na ma’aikatar kuɗi da Ladidi Ibrahim Garko ta ma’aikatar al’adu da yawon buɗe ido da Baba Halilu Dantiye na ma’aikatar watsa labarai da Shehu Aliyu Yammedi na ma’aikatar ayyuka na musamman da Abbas Sani Abbas na ma’aikatar raya karkara.

Sanarwar ta ce gwamnan ya yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati, da kuma taimaka wa gwamnan wajen kai romon dimokuraɗiyya ga ƴan jihar.

Kazalika gwamnan ya yi wa wasu kwamishinonin sauyin ma’aikatu, waɗanda suka haɗa da: “mataimakin gwamnan jihar, wanda aka sauya masa ma’aikata daga ƙananan hukumomi zuwa ma’aikatar ilimi mai zurfi, da Mohammad Tajo Usman daga ma’aikatar kimiyya da fasaha zuwa ma’aikatar ƙananan hukumomi, da Dr Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata daga m’aikatar ilimi mai zurfi zuwa kimiyya da fasaha.”

Sauran sun haɗa: “Hajiya Amina Abdullahi daga ma’aikatar jinƙai da rage talauci zuwa ma’aikatar mata, da Nasiru Sule Garo daga ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman da Haruna Doguwa daga ma’aikatar ilimi zuwa ma’aikatar albarkatun ruwa da Ali Haruna Makoda daga ma’aikatar albarkatun ruwa zuwa ma’aikatar ilimi da Aisha Lawal Saji da aka mayar m’aikatar al’adu da yawon buɗe ido.”

Matuƙa Adaidaita Sahu za su dawo biyan haraji a Kano.

Malaman Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Kano sun tsunduma Yajin Aiki.

Rikicin Siyasa Na Kara Yin Zafi A Jam`Iyyar NNPP Yayin Da Kwankwasiyya Ke Rasa Jiga-Jigai.

Sai dai gwamnan ya buƙaci waɗanda aka cire ɗin su je ofishinsa domin a ba su wasu ayyukan daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *