April 5, 2025

SANATA ABDUL’AZIZ YARI YA BA KUNGIYAR YAN JARIDA TA KASA RESHEN JAHAR ZAMFARA SABUWAR MOTA.

Daga Sani Ibrahim Maitaya

Sanata Abdulaziz Yari Abubakar (Marafan Sokoto), mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, ya nuna alhinin sa ga mambobin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) reshen jahar Zamfara, sakamakon wani hatsarin mota da ya rutsa da motar su mai daukar mutane 18.

A yayin wani taron manema labarai inda ya yi jawabi kan kalubalen tsaro da yanayin siyasar Zamfara, Sanata Yari ya jajanta wa ‘yan jaridun dangane da hadarin da ya faru a ranar 29 ga watan Nuwamba 2024, wanda ya hada da mambobin kungiyar su goma sha biyar bayan taron da aka gudanar a Owerri jahar Imo.

Sakamakon hakan Sanata Yari ya sanar da bayar da sabuwar motar bas nan take domin ganin ‘yan jaridar sun ci gaba da gudanar da ayyukan su ba tare da wata matsala ba. Ya kuma yi addu’ar Allah ya kiyaye da kuma kare afkuwar al’amura a nan gaba.

Sanatan ya samu cikakken bayani game da hatsarin daga Hon. Ibrahim Muhammad Birnin Magaji tsohon shugaban kungiyar NUJ ta jahar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *