Sanatar da aka dakatar mai wakiltar yankin Kogi ta tsakkiya Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta gabatar da hujjoji don tabbatar da zargin cin zarafi ta fuskar jima’i da ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio.
Natasha ta bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da ita a shirin “Politics Today” na gidan talabijin din Channels da yammacin ranar Alhamis.
Ta dage cewa za ta gabatar da hujjojin a lokacin da ya dace da kuma wurin da ya dace.
“A daidai lokaci da kuma dai-dai wuri, zan gabatar da hujjojin da nake da su,” in ji ta.
Bayanin na ta na zuwa ne bayan fiye da wata ɗaya da ta bayyana a talabijin na kasa cewa, dalilin rikicinta da Shugaban Majalisar Dattawa ya samo asali ne daga kin amincewar ta da bukatun jima’i da ya nemi yi da ita.
Ta kara da cewa ƙin amincewar ta ya sa aka fara ƙoƙarin hana ta damar gabatar da ƙudurori da suka shafi Kamfanin Karafa na Ajaokuta da ke jihar Kogi.
Natasha ta kuma yi tsokaci kan matakin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dauka, na ƙin amincewa da koke da ke neman a janye ta daga Majalisar Dattawa, inda ta bayyana matakin a matsayin wanda ya dace kodayake an yi jinkiri akan shi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rasuwar Sheikh Idris: mun “fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki”- Gwamnan jihar Bauchi.
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP