Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Mai martaba Sarkin Agwada a jihar Nasarawa, Alhaji Abubakar Sadiq Obagu, ya buƙaci gwamnatin tarayya ta sauke Kwamanda Attah John Onoja tare da tawagarsa daga cikin al’ummarsu saboda gaza daƙile ayyukan haƙar ma’adanan da ba bisa ka’ida ba a yankin Rafin Gabbas, wanda ke haddasa mutuwar matasa da yara a yankin.
Leadership ta rawaito Sarkin ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi gungun masu zanga-zangar al’umma a fadarsa a ranar Litinin, ya ce mazauna garin sun daina samun damar zuwa gonakinsu saboda barazana da tsangwama daga jami’an tsaron ma’adanan.
> “Tun da aka fara wannan haƙar ba bisa ka’ida ba, mun yi rashin mutane da dama yara da manya. Yanzu ma, jami’an Mining Marshal na hana mu wuce wa wajen gonaki, suna kama mutane ba tare da wani dalili ba.”
Ya ƙara da cewa kimanin jami’ai 50 na Mining Marshal ne ke tsare wuraren da ake haƙar ba bisa ka’ida ba, kuma ana amfani da ƙananan yara a wuraren haƙar da daddare.
Sarkin ya bayyana cewa ya riga ya rubuta takarda zuwa ga Shugaban Hukumar Mining Cadastre na ƙasa in da ya bayyana rashin amincewar al’umma ga kamfanonin da ke da’awar lasisi a yankin.
Ya roki Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da su kawo ƙarshen wannan fitina.
Martanin Kwamandan Mining Marshal
A nasa bangaren, Kwamanda Attah John Onoja, ya ce aikinsa shi ne kare dukkan wuraren hakar ma’adanai, kuma yana bin dokoki wajen cafke masu laifi.
> “Mun kama masu haƙar ba bisa ka’ida ba kuma mun gurfanar da su gaban kotu. Wannan batu ne mai sarkakiya wanda ya shafi miyagun ayyuka da dama”