Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Mohammad Abubakar II ya musanta maganar da ake yi cewa
sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnoni.
Sarkin musulmin ya ce sarakunan gargajiya sun kasance jagorori a ƙasar tun kafin ta samu ƴancin
kai, sannan ya ƙara da cewa sarakunan sun fi gwamnonin fahimtar yanayin ƙasar.
BBC Hausa ta rawaito, ya bayyana hakan ne a wani taro na ƙungiyar cigaban matasan arewacin Najeriya da Gidauniyar Tunawa da Sardauna ta shirya a Abuja a ranar Talata.
An Yi Kira Ga Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci Kan Ta’amali Da Miyagun Kwayoyi.
Ƴansanda Sun Kama Wani Ɗan Kasar Aljeriya Da Bindigu A Zamfara.
Gwamnan Jigawa ya janye dakatarwar da ya yi wa kwamishinansa kan zargin lalata.
Tun da farko, tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya suna
tsoron gwamnoni.
Da yake mayar da martani, sarkin na Musulmi ya ce, “Na ji an ce sarakunan gargajiya na tsoron gwamnoninsu. Ba haka ba ne, sarakuna ba sa tsoron gwamnoni. Sarakunan gargajiya suna girmama kansu ne, sannan suna girmamma gwamnonin domin suna da iko a jihohinsu.
“Duk lokacin da wani abu ya faru, muna mayar da shi zuwa ga Allah ne. Muna kawo sauyi, kuma muna karɓar sauyi a yadda suka zo mana. Duk mun sani,
akwai sarakunan gargajiya a Najeriya tun a shekarar 1824, amma a shekarar 1960 ce Najeriya ta samu ƴanci.”
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.