Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga gwamnonin jihohi a fadin Najeriya da su dauki tsarin shugabanci na hada kai da Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ke aiwatarwa, ta hanyar kawar da bambanci tsakanin ‘yan asalin jiha da wadanda ba ‘yan asalin jahar ba.
Sarkin Musulmin ya yi wannan kira ne a ranar Talata, yayin da ya kai ziyarar barka da Sallah ga gwamnan a dakin taro da ke masaukin shugaban kasa dake Sokoto.
Ya jaddada cewa a jihar Sokoto, duk ‘yan Najeriya ana daukar su a matsayin ‘yan asalin jiha ɗaya, wanda hakan ke kara hadin kai da jin dadin zama ga mazauna yankin.
“A Sokoto, ba mu raba mutane da sunan ba ‘yan asali ba; sai dai mu dauke su a matsayin ‘yan uwa da mazauna cikin al’umma, ɗaya” in ji Sarkin Musulmi.
Ya bukaci sauran jihohi da su dauki wannan tsari domin karfafa zaman lafiya, hadin kai, da dunkulewar kasa wuri ɗaya.
Mai alfarma Sarkin Musulmi ya kuma jaddada muhimmancin rawar da gwamnonin jihohi ke takawa, wajen tabbatar da tsaro da walwalar al’ummar su, yana mai cewa babu ci gaba a cikin al’umma ba tare da tsaro ba.
“Muna gode wa kokarin gwamna a Sokoto, kuma mu a matsayin mu na sarakunan gargajiya, za mu ci gaba da marawa shirye-shiryen sa baya domin cigaban jihar mu.
“Gwamnan tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro, sun taka rawar gani wajen inganta tsaro da dakile ayyukan ‘yan bindiga a jihar,” in ji shi.
Har ila yau ya yabawa gwamnan bisa rabon kayan abinci da ya yi a lokacin azumin Ramadan, yana mai cewa hakan bai taba faruwa a tarihin jihar Sokoto ba.
A nasa bangaren Gwamna Aliyu ya jaddada kudirin gwamnatin sa na tabbatar da tsaro da jin dadin al’ummar jahar.
Ya bayyana rashin aikin yi musamman tsakanin matasa a matsayin ummul haba’insin rashin tsaro a fadin kasar nan, yana mai bayyana cewa matasa da yawa sun zabi zama masu tsegunta bayanai ga kungiyin ‘yan ta’adda sakamakon rashin kudi.
Ya kuma bayyana shirin sa na fadada ayukkan koyar da sana’o’in hannu, domin shigar da matsa marassa aikin yi a ciki.
Gwamnan ya tabbatar da aniyar gwamnatin sa wajen taimakawa harkokin addinin musulunci, yana mai bada tabbacin cewa, masallatai da makarantun islamiyya zasu ci gaba da samun gudummuwar gwamnati.
Ya kuma bayyana godiyar shi ga al’ummar jahar Sokoto bisa ga ci gaba da bayar da goyon baya da addu’a da suke yi, yana mai kira ga resu da su ɗore da hakan.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta ficewar Nijar daga rundunar hadin gwiwa ta MNJTF.
-
CBN ya ƙaryata fitar da takardun kuɗi ƴan dubu 5 da dubu 10
-
Gwamnatin jihar Kebbi ta musanta yi wa ƴan luwaɗi da maɗigo rajista a jihar.
-
Ɗan banga ya harbe kansa a ƙoƙarin bin wanda ake zargi da aikata laifi a Abuja.
-
Sojojin Najeriya sun yi nasarar rage ayukkan ƴan ta’adda a jihohin Kebbi da Zamfara.