Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya gargadi sarakunan gargajiya a jahar da su daina mamayewa da kwace filaye ba bisa ka’ida ba a yankunan su.
Ya yi wannan gargadi ne a lokacin gaisuwar Sallah ta Eid-el-Fitr da aka gudanar a fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya.
Gwamna Sani ya bayyana cewa gwamnatin jihar, tana karbar koke-koke kan yadda dagatai da masu unguwanni ke kwace filaye ba bisa doka ba.
Ya jaddada cewa duk filaye mallakin gwamnati ne, don haka wajibi ne a bi doka da ka’ida wajen mallakar su daga hukumomin da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Gwamnan wanda Alhaji Muktar Shehu Jarman Zazzau mai ba shi shawara kan harkokin masarautu ya wakilta, ya kuma bukaci sarakunan gargajiya da su ci gaba da tabbatar da kiyaye zaman lafiya a yankunan su da kuma jihar baki daya.
Haka kuma, ya bukaci manoma da su koma gonakin su domin matsalar tsaro ta inganta a jihar.
Tun da farko Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya sake nanata umarnin sa ga hakimmai, dagatai da masu unguwanni, da su guji zaluntar jama’ar su.
Ya kuma gargade su da kada su hada baki da masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, wadanda ke kokarin gudanar da haramtattun ayyuka a yankunan su.
Sarkin ya bayyana cewa kafin a ba wa wani damar gudanar da ayukkan hakar ma’adinai, dole ne a tabbatar da sahihancin sa daga hukumomin da suka dace, sannan a sanar da masarauta.
Bamalli ya gargadi dagatai da su daina mamayewa da raba filayen da ke karkashin Ma’aikatar kula da gandun daji, inda ya bukace su da su tsaya kan kadarorin da ke karkashin masarautar su kadai.
Ya kuma tunatar da duk masu rike da sarauta biyu su ajiye daya daga ciki, bisa ga yadda gwamnatin jihar ta umarta.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP
-
Babu wani gurbi a gidan gwamnatin Delta cewar Dennis Guwor ga ƴan takarar gwamnan jihar.