Nijeriya ta bukaci masu hannu da shuni a fadin duniya da su tallafawa kasashen Afrika da sauyin yanayi ya shafa.
Mataimakin shugaban majalisar wakilai ta kasa, Benjamin Okezie Kalu kuma shugaban tawagar Nijeriya a ci gaba da zaman majalisar wakilai daga kasashen Afrika dake gudana a kasar Afrika ta Kudu a ranar Talata inda ya bayyana matsayar kasar.
Da yake jawabi kan makalar da aka gabatar mai taken “Tasirin sauyin yanayi da tsarin Afrika na zuwa COP”, wanda daraktan shirye shirye da bincike na PACJA, Mista Charles Mwangi Nyambura ya gabatar, Kalu ya bada shawarar karbar haraji kan sauyin yanayi a kasashe masu rauni na Afrika.
Mataimakin shugaban majalisar, wanda ya koka kan ambaliyar ruwa da ta faru a jihar Borno da Zamfara ya ce shawarar harajin na sauyin yanayi zai taimaka wajen rage radadin da sauyin yanayi ya haifar a yankin.
Ya ce: ” Afrika ta tasirantu da illa na sauyin yanayi duk da cewa tana bada kashi 3.8 ga batun fitar da iskar idan aka kwatanta da kasar China dake fitar da kaso 23 da kasar Amurka mai fitar da kaso 19 da Turai mai kaso 13.
“Sauyin yanayi ya hana Afrika samun ci gaba da fimma muradin karni gami da walwalar mutane.
” A yau, kusan ‘yan Afrika Miliyan 600 basa samun wutar lantarki kamar yadda Bankin duniya ya fada”.
Jagoran na tawagar Nijeriya ya kuma bayyana illar da karancin abinci ke yi wanda sauyin yanayi ya haifar.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.