Kungiyar Kare tattalin arziki (SERAP) ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya ƙi amincewa da bashin dala biliyan $1.08 da Bankin Duniya ya amince da shi kwanan nan, maimakon haka ya umarci Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a Mista Lateef Fagbemi SAN, da kuma hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin bacewar fiye da Naira biliyan 233 da aka karkatar da su, ko kuma ba a bayyana inda suka shiga ba daga hannun Kamfanin Kasuwancin Wutar Lantarki na Najeriya (NBET) Abuja, da wasu ma’aikatun gwamnati, sassa, da hukumomi (MDAs).
SERAP ta ce duk wanda ake zargi da hannu a wannan lamari ya kamata a gurfanar da shi a gaban kuliya idan akwai shaidun da suka wadatar, sannan a dawo da duk wasu kuɗi da suka ɓace zuwa baitul mali.”
A cewar SERAP, a yi amfani da wannan Naira biliyan 233 da aka dawo da su don cike gibi a kasafin kuɗin 2025 da kuma rage nauyin bashin da ke addabar Najeriya.
A makon da ya gabata ne Bankin Duniya ya amince da bashin dala biliyan 1.08 ga Najeriya da nufin inganta ilimi, ƙarfafa iyalai da al’ummomi, da kuma kyautata abinci mai gina jiki ga ƙungiyoyin da ba su da isasshen samun tallafi.”
SERAP ta ce bashin Bankin Duniya ba dole ba ne kuma ba shi da amfani ga al’umma, musamman idan aka yi la’akari da nauyin bashin da ke kan ƙasa da kuma yawancin kuɗaɗen jama’a da suka ɓace daga ma’aikatu da hukumomi da sassan gwamnati, wanda gwamnatin ta kasa bincika ko dawo da su.
A cewar SERAP “Bai kamata Gwamnatin tarayya ta ɗauki wani bashi daga Bankin Duniya ko wata hukuma ba, har sai an dawo da Naira biliyan 233 da suka ɓace, dai-dai da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (da aka gyara) da kuma alkawurran ƙasa da ƙasa kan yaƙi da cin hanci.”
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya
-
Ƴansandan Najeriya sun ƙi karɓar cin hancin naira miliyan 1 jihar Katsina sun kuma cafke waɗanda ake zargin
-
Me ya sa ƴan Majalisar Wakilai su ka gayyaci Gwamnan riƙon ƙwarya na jihar Rivers?
-
Abin da ya sa Matatar Dangote rage farashin Man Fetur
-
Kotu a Kano ta ɗage yanke hukunci kan shari’ar da ake yi wa tsohon Gwamnan jihar Ganduje