An shawarci mabiya addinin Musulunci da su kasance jakadu na gari a cikin dukkan harkokin su.
Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ne ya bayar da wannan shawara, yayin gabatar da jawabi a taron shekara-shekara karo na 27 na ƙasa (Muslim Umma Convention), wanda aka gudanar a sansanin Alhazsai na Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar da ke jihar Bauchi.
Yayin da yake magana kan jigon taron mai taken: “Kalubalen da Musulmi ke fuskanta a Najeriya: Hanyar Magance su,” Shekarau ya jaddada cewa “Addinin Musulunci addini ne na ilimi, kuma ilimi yana jagorantar ɗabi’u nagari.
Ya ce “Ba za ka iya zama a kujerar mulki kana ikirarin kai Musulmi ne ba, amma kuma ana danganta ka da jagoranci marar kyau.”
Taron ya bayar da dama ta musamman ga shugabannin Musulmi da malaman addini, na su taru domin tattaunawa kan hanyoyin samar da zaman lafiya, dai-daito, da cigaba a cikin al’umma.
Shi ma da yake gabatar da jawabi na musamman Shugaban Umma na kasa Farfesa Muhammad Babangida, ya bayyana wasu daga cikin ayukkan da ƙungiyar Umma ke gudanarwa, yana mai cewa “Kungiyar Umma na aiki tukuru wajen inganta ilimin addinin Musulunci, kare adalci a cikin al’umma, da bayar da taimakon jin kai ga masu bukata.”
Ya ƙara da cewa kungiyar na aiki kafada da kafada da hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki, don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.
Farfesa Babangida ya jaddada buƙatar samun haɗin kai tsakanin Musulmi, domin cimma burin ci gaban al’umma da jin daɗin ta.
Ya kuma buƙaci mahalarta taron da su gudanar da tattaunawa mai ma’ana tare da fitar da hanyoyin magance matsalolin da Musulmi ke fuskanta a Najeriya.
A nasa ɓangaren yayin da yake ƙaddamar da buɗe taron, Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed wanda mataimakin sa Auwal Jatau ya wakilta, ya bayyana muhimmancin haɗin kai da haɗa hannu a tsakanin Musulmi, wajen fuskantar matsalolin da ke addabar al’umma.
Ya bayyana cewa “Gwamnatin jihar Bauchi tana mayar da hankali kan ilimi, ba matasa dama, da kuma tattaunawar addinai domin gina al’umma mai adalci da dai-daito.”
Jatau ya yaba wa masu shirya taron bisa zaɓar Bauchi a matsayin masaukin taron, inda ya bayyana taron a matsayin muhimmin dandali na tattaunawa.
Jaridar Arewa PUNCH ta ruwaito cewa, taron ya samu halartar sarakunan gargajiya, jami’an tsaro, da manyan jami’an gwamnati, inda suka gudanar da muhawara mai ma’ana kan matsalolin da Musulmi ke fuskanta a faɗin ƙasar.
Taron ya ba da dama ga masu ruwa da tsaki su tattauna hanyoyin magance matsaloli, da tsara sabon tafarki domin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaba tsakanin Musulmi a Najeriya.