September 22, 2021

Shirin Aiki Da Ilimi Fitowa Na (13)

Page Visited: 290
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 42 Second

Daga: Sakibu Muhammad Adam

FASSARAR LITTAFIN ASHMAWI

A yau in sha Allahu zamu dora akan sunnonin wanka
Malam yace: amma sunnoni wanka guda hudune (4)

wanke hannaye izuwa gwiwar hannunsa
kuskurar baki
shaqa ruwa a hanci
wanke kafar kunne (maana: shafa) anan malamai sukace: wannan shine abin da aka sunnanta shafarsa ba wankeshiba.
Amma abin da yake ya fita daga kafar kunne (bayan kunne kenan) wannan yana daga abin da ya wajaba a wankeshi.

Mai wanka zai kula wajan shafar kafar kunnensa kada ya shigar da ruwa cikin kunnensa gudun kada ya cutar dashi.

MUSTAHABBAN WANKA

Malam yace: amma mustahabban wanka guda shidane

farawa da gusar da najasa daga jikinsa.
(Bayan yayi niyya ya wanke hannayensa sau uku, sai ya dibi ruwa ya wanke daga cibiyarsa izuwa gwiwarsa duk inda najasar take.

sannan ya wanke gabban alwararsa har izuwa qafafuwansa (ma’ana: ya cika alwala kamar yadda zaiyi alwarar sallah)

ya wanke saman jikinsa kafin qasan jikinsa (kuma ya fara da bangaren dama.

ya wanke kansa sau uku kamar yadda yazo a sunna ta Shugaba SAW a hadisin Nana Aisha RTA “أن النبي (ص) كان إذاغتسل من الجنابة بدأ فغسل يديه، ثم توضأ كما يتوضأ للصلاة، ثم يدخل أصابعه الماء فيخلل بها أصول شعره، ثم يصب على رأسه ثلاث غرف، ثم يفيض الماء على جسده كله” ma’ana: “Annabi SAW ya kasance : idan zaiyi wankan janaba yana faraway da wanke hannayensa, sannan yayi alwala kamar yadda zaiyi alwalar sallah, sannan ya debi ruwa da hannanyensa ya cuccuda gashinsa, sannan ya kamfaci ruwa sau uku ya zuba a kansa, sannan ya kwara ruwa a jikinsa gaba daya”.

farawa da bangaren damansa kafin bangaren hagu. Kamar yadda yake a sunna ta Annabi SAW cewa كان يعجبه التيمن cewa damaitawa tana qayatar da Annabi acikin dukkan lamuransa.

karanta ruwa, ma’ana: ya qaranta ruwa ba tare da barnad ruwa ba a yayin wanka Amma kuma ya tabbatar da ya kyautata wankansa bai bar wani waje da bai wanke ba.

Nan shine qarshen bayani akan abin da ya shafi wanka. Sai Allah ya hadamu a darasin gaba.
الحمد لله

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us