December 2, 2021

SHUGABA BUHARI YAYI JIMAMIN RASUWAR HALIMA ABDULSALAM WACCE TAYI ZARRA GURIN WA’AZANTAR WA.

Page Visited: 436
0 0
Read Time:48 Second

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan Sananniyar Malaman Addinin Musulunci, Malama Halima Shittu Abdulsalm, Mai Dakin Fitaccen Malami mai Wa’azi Sheikh Abdulwahab Abdallah Muhammad.

Mallama Halima, wacce ta rasu a Kano ta taimaka matuka gaya gurin wayar dakai kan addinin musulunci a ciki da wajen kasarnan.

Cikin sakon Ta’aziyya ga Sheikh Abdulwahab Abdalla, Shugaba Buhari yache ya damu matuka a bisa Rasuwar Malamar.

Acikin Sakon Shugaban Kasa Muhammad Buhari ga Malamin, ” Marigayiya Mai Dakin ka ta shafe yawancin Rayuwar ta tana koyar wa da Wa’azantar da Addinin Islama. Rashin ta ba rashi ne kawai ga Iyalin ka ba ga kasa ne baki daya, Za’a rika tunawa da ita a fannin shirye shiryenta a kafafen Rediyo da Telabijin daga baya bayan nan kuma a kafofin yada labaru na zamani da sakonni wayar dakai gameda musulunci wanda kuma mabiyan ta suka amsa sosai. Tayi Zarra gurin wa’azantar wa, “.

Shugaba Buhari Yayi Addu’a Allah yajikanta da Rahma ya kuma baiwa iyalanta hakurin rashinta.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *