Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da wani babban kwamiti don sa ido kan shirye-shiryen kidayar jama’a da gidaje ta kasa mai zuwa, tare da umarnin a gabatar da rahoton farko cikin makwanni ukku.

Martaba FM dake kan yanar gizo ta ruwaito cewa, hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin watsa labarai da tsare-tsare Bayo Onanuga ya fitar a ranar Laraba.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu.

Kwamitin mai mambobi takwas na ƙarƙashin jagorancin Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki Sanata Atiku Bagudu; Sauran mambobin sun haɗa da Ministan Harkokin Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arzikin Ƙasa, Shugaban Hukumar Harajin Cikin Gida ta Ƙasa (FIRS), Darakta Janar na Hukumar Kula da Shaidar zama dan Ƙasa (NIMC), Babban Sakatare na Shugaban Ƙasa, da Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Gudanarwa da Ayyuka (Ofishin Shugaban Ma’aikata).

A jawabin sa, Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin gudanar da sahihiyar kidaya da za ta dogara da fasahar zamani domin ci gaban kasa, da ingantattun tsare-tsare da tsarin manufofi a muhimman bangarori kamar ilimi, kiwon lafiya da tsaro.

“Muna sa ran za ku tabo fannin fasaha saboda kidayar dole ta kasance mai dogaro da fasahar zamani. Al’amurra sun sauya tun lokacin da aka gudanar da aikin karshe. Lissafi dole ya dogara da fasaha ta zamani, tare da amfani da bayanan biyometrik.” in ji Shugaban kasa.

Ya kara da jaddada mahimmancin samun kuɗi, yana ƙarfafa kwamitin da ya binciko hanyoyin samun kuɗaɗe daga ciki da wajen ƙasa. Ya umurci Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki da ta jagoranci haɗin guiwa da hukumomin da suka dace.

Sanata Bagudu ya tabbatar wa da Shugaban ƙasa cewa kwamitin ya shirya tsaf don miƙa rahoton cikin wa’adin da aka bayar. Ya tuna da umarnin da Shugaban ƙasa ya bai wa ministoci a baya cewa su kasance masu ƙirƙira da kuma amfani da albarkatun da ake da su, koda kuwa akwai ƙalubalen tattalin arziki.

Ministan Yada Labarai Mohammed Idris wanda shi ma mamba ne a cikin kwamitin, ya bayyana cewa samun sahihan bayanai masu tabbaci yana da matuƙar muhimmanci wajen tsara shirye-shirye da isar da ayukka a dukkan fannoni.

A nasa jawabin a wurin taron, Shugaban Hukumar Kidaya ta Ƙasa (NPC) Nasir Isa Kwarra wanda zai kasance sakataren kwamitin, ya bayyana cewa Hukumar ta fara aiwatar da shirye-shiryen kidayar tare da haɗin guiwa da masu ruwa da tsaki.

Kwarra ya jaddada aniyar Hukumar wajen gudanar da sahihiyar kidaya da za ta kasance ta gaskiya kuma mai amfani da fasahar zamani, domin tallafawa tsare-tsaren ci gaba na ƙasa.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *