Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu, zai wuce ƙasar Afirka ta Kuda daga ƙasar Faransa a ci gaba da ziyarar aiki da ya ke yi.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce Shugaba Tinubu zai zarce Afirka ta Kudu ne a gobe Litinin, domin ya jagoranci taron kwamitin haɗin kai tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 11 tare da shugaba Cyril Ramaphosa.
“Taron wanda aka shirya gudanarwa a ranar Talata, 3 ga Disamba, zai kasance gabanin taron ministocin ƙasashen a ranar 2 ga Disamba, 2024, a zauren
majalisar dokokin Afirka ta Kudu da ke birnin a Cape Town”, in ji Onanuga.
ASUU ta nuna damuwa kan yawaitar ɗaliban da ke samun sakamakon first-class a Najeriya.
NAHCON ta ce kowanne alhajin 2023 za a mayar masa da naira 60,080.
Sanarwar ta ci gaba da cewa shugabannin biyu za tattauana batutuwa da dama da suka shafi dangantakar ƙasashen biyu da batutuwan da suka shafi Afirka da ƙasashen duniya.
“Shugabannin za su ɗora kan alƙawuran da suka yi a ranar 20 ga watan Yuni, 2024, a ganawar da suka yi a birnin Johannesburg jim kaɗan bayan rantsar da shugaba Ramaphosa a wa’adin mulki na biyu”, in ji sanarwar.
A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya tafi ziyarar aiki ta kwana uku zuwa ƙasar Faransa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Tsohon mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya Christian Chukwu ya rasu
-
EFCC ta gurfanar da wasu mutum biyu kan zargin damfara da sunan A’A Rano
-
APC ta rufe hedkwatarta da ke Abuja.
-
An hallaka mutum 1 wani kuma ya jikkata kan zargin satar kare a jihar Bauchi.
-
Ɗiyata “ta yi aiki wa Buhari shekaru huɗu a ofishin Osinbajo ba tare da ko kwabo ba-Buba Galadima