Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa za a saka Bitcoin, Ethereum, XRP, Solana, da Cardano a cikin sabon shirin ajiyar kudaden intanet na kasar (US Crypto Strategic Reserve).
Trump ya bayyana wannan shiri a wani saƙon da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta mai suna Truth Social a ranar Lahadi, yana mai cewa wani kwamitin aiki na fadar shugaban kasa ya samu umarni don ci gaba da kirkirar shirin.
Ya bayyana cewa manufar wannan mataki ita ce karfafa matsayi na Amurka, a kasuwar kuɗaɗen intanet ta duniya da kuma bunƙasa masana’antar crypto.
“Ajiyar Kudaden Crypto na Amurka zai daga darajar wannan masana’anta mai muhimmanci bayan shafe shekaru ana kai mata hare-hare karkashin gwamnatin Biden. Saboda haka Dokar Shugaban Kasa kan Kudaden Intanet ta umarci Kwamitin Aiki na Shugaban Kasa da su ci gaba da kafa Crypto Strategic Reserve da ke dauke da XRP, SOL, da ADA,” in ji Trump.
Ya kara da cewa “Zan tabbatar da cewa Amurka ta zama cibiyar crypto ta duniya. Muna sake maidawa Amurka darajarta!
“Kuma ba shakka, BTC da ETH, a matsayin manyan kudaden crypto masu kima, za su kasance a tsakiyar wannan ajiyar. Ina son Bitcoin da Ethereum!”
A watan Disamba Trump ya nuna goyon bayan sa ga masana’antar crypto, inda ya bayyana shirin sa na kafa wata ajiyar bitcoin ta Amurka.
“Za mu yi wani abu mai girma da crypto saboda ba ma son China ko wani ya fi mu gaba… wasu sun rungumi crypto, mu kuma muna son kasancewa a gaba,” in ji Trump a wata hira da CNBC.
Lokacin da aka tambaye shi ko Amurka za ta kafa ajiyar Bitcoin irin ta man fetur (Strategic Petroleum Reserve), Trump ya amsa da cewa, “Eh, ina ganin haka.”
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.
-
Kswanaki biyu bayan rasa ran wasu mutum 16 a wani hatsarin mota a Abeokuta wasu ukun sun sake rasuwa in da wasu suka jikkata.