August 8, 2022

Shugaban Hukamar Karota Na Jihar Kano Ya Kasa Bayyana A Gaban Kotu.

Page Visited: 378
0 0
Read Time:34 Second

Daga: Suleman Ibrahim Moddibo

Wata kotun majistiri da ke zama a gidan Murtala a birnin kano karkashin jagorancin mai shari’a Muhammad Jibril ta umarci shugaban hukumar Karota na Baffa Babba Dan Agundi da ya bayyana a gabanta a zamanta na ranar 19 ga watan Oktoba, na shekarar 2020 sakamakon rashin bayyanar da yayi yau a gabanta.

Baffa Babba Dan Agundi ya gaza bayyana gaban kotun ne a zamanta na yau Laraba, 30 ga watan Satumba, saidai lauyoyinsa sunce suna da suka kan gayyatar da aka yi masa.

Tun farko dai wasu masu sana’ar adaidata sahu a jihar Kano ne suka shigar da karar Dan Agundi gaban kutun bisa zargin yi musu zamba cikin aminci.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *