Jami’an Rundunar Sojojin Ruwa na Najeriya da ke sansanin Epe Jihar Legas, sun dakile wani yunkurin fasa kwauri a kan hanyar Epe-Ijebu-Ode
Mataimakin Shugaban Sansanin Sojojin Ruwa Kwamanda Chukwudi Atuba, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikawa PUNCH a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa a ranar 22 ga watan Janairu, jami’an tsaro sun samu bayanan sirri kan wani yunkurin safarar haramtattun kaya, in da tawagar sintiri ta yi gaggawar ɗaukar mataki tare da daƙile fasa kwaurin.
A cewar sa, an kama motoci shida ɗauke da shinkafar waje da aka shigo da ita, yayin da waɗanda ake zargi suka tsere suka bar kayan su.
Ya ƙara da cewa kayan da aka kama wato buhuna 213 na shinkafar waje, an mika su ga Hukumar Kwastam ta Najeriya don ɗaukar matakin da ya dace.
Atuba ya bayyana cewa mika kayan da aka kwace an yi shi ne ta hannun Navy Lieutenant AS Bello, wanda ya damka buhunan shinkafar ga Mataimakin Kwanturola Odoemenah, mai wakiltar Kwanturola.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.
-
Kswanaki biyu bayan rasa ran wasu mutum 16 a wani hatsarin mota a Abeokuta wasu ukun sun sake rasuwa in da wasu suka jikkata.