Wasu da ake zargin ‘yan bindiga da ake kira ‘yan ta’adda na Lakurawa sun kai hare-hare a kan kauyuka biyar, da ke yankin ƙaramar hukumar Arewa a Jihar Kebbi, in da suka kashe akalla mutum 10 tare da jikkata wasu da dama.
Majiyoyin sirri sun shaida wa Zagazola Makama cewa kauyukan da harin ya shafa sun haɗa da Birnin Debi, Garin Nagoro, Yar Goru, Dan Marke, da Tambo.
‘Yan ta’addan sun dira kauyukkan da misalin karfe 8:48 na yamma a ranar 9 ga watan Maris 2025, in da suka banka wa gidaje wuta tare da harbin kan mai uwa dawabi. Daya daga cikin waɗanda suka rasu shi ne Garba Maigari mai shekaru 50, yayin da ba a tantance sunayen sauran mutum tara da suka mutu ba.
An kai wasu daga cikin waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Tarayya ta Birnin Kebbi domin samun kulawar likita, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan domin tantancewa.
A martani ga harin, dakarun sojojin Najeriya, ‘yan sanda, da ‘yan banga sun isa yankunan da abin ya shafa, kuma rahotanni sun nuna cewa zaman lafiya ya dawo a yankin.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya