Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Dakarun sojojin da aikin soji na musamman na ‘Operation SAFE HAVEN’ sun sanar da kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato da ke arewacin Najeriya.
BBC ta rawaito, a wata sanarwa da kakakin aikin na Operation Safe Haven, Samson Nantip Zhakom, ya fitar, ya ce, “sojojin sun kai farmakin ne a maɓoyar masu garkuwa da mutanen, inda suka samu nasarar kama wasu ƴanbindiga a yankin Rafiki.
Babban hafsan Sojin ƙasa ya sha alwashin kawo ƙarshen Ƴan ta’addan Lakurawa cikin kankanin lokaci.
Jami’an tsaro sun ceto manoma 36 daga hannun ƴan bindiga a Kebbi.
Ya ce sun kuma kama alburusai guda 439 da wasu makamai.
Sanarwar ta ƙara da cewa sun yi aikin na musamman domin tabbatar da mutane sun samu sukunin gudanar da hidindimun kirsimeti da sabuwar shekara.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƴansanda sun kama mutane 7 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne a Ogun.
-
Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.
-
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
-
Mun mayar da yara miliyan 1.5 makaranta a Borno – Zulum.
-
Bankin Duniya ya ce har yanzu Najeriya ba ta kama hanyar yaƙi da rashawa ba.