A ci gaba da aikin “Operation FANSAR YANMA” da rundunar sojin Najeriya ke gudanarwa, dakarun sun samu nasarar ceto mutane 50 da kuma dawo da shanu 32 da aka sace a ƙauyen Raudama da ke ƙaramar hukumar Faskari, jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen da yammacin ranar Lahadi, 27 ga Afrilu, 2025, in da su ka yi garkuwa da mazauna ƙauyen tare da sace shanun su.
Wani masanin tsaro daga Maiduguri kuma kwararre kan yaƙi da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana cewa farmakin ya auku ne da misalin karfe 8 na dare, yayin da ‘yan bindigar suka kutsa ƙauyen da muggan makamai.
Dakarun soji tare da haɗin gwiwar ƴansanda sun yi gaggawar kai ɗauki, in da suka bi sahun ƴan bindigar cikin daji. Bayan fafatawa mai zafi, dakarun sun yi galaba a kansu, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
Rundunar ta ceto dukkanin mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da karɓe duka shanun da aka sace, a cewar rahoton.
Yankin Arewa maso yammacin Najeriya dai ya daɗe ya na fama da matsalar rashin tsaro in da ƴan bindiga ke farmakar garuruwan da ke yankin karkara, suna kashe su tare da yin garkuwa da sace dabbobinsu, lamarin da hukumomin ƙasar ke cewa suna yin aiki domin kawo ƙarshen matsalar.