Dakarun sojin Najeriya sun kawar da babban masanin hada bama-baman Boko Haram Amirul Bumma, tare da wasu ‘yan ta’adda takwas yayin wani farmaki na share sansanonin ‘yan ta’adda a dajin Sambisa Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa wannan farmaki ya faru ne a Karamar Hukumar Bama, a lokacin aikin tsaftace daji na hudu.
Punch ta rawaito, Babban Kwamandan Rundunar Sojojin runduna ta bakwai Manjo Janar Abubakar Haruna, ya yaba da jajircewar sojojin tare da nanata kudirin rundunar soji, na kawar da ta’addanci a Arewa maso Gabas da ma Najeriya baki daya.
Majiyoyin sojoji sun tabbatar da cewa dakarun runduna ta 21, da jami’an bataliya ta musamman ta 199, tare da JTF da wasu sojojin haɗin gwiwa ne suka kaddamar da farmakin, bayan samun bayani kan yadda ‘yan ta’adda ke sake shiryawa a wani sansani mai ƙarfi tsakanin Sabil Huda da Njimiya, kusa da Alai Dala Stand.
‘‘Yan ta’addan sun yi yunkurin mayar da martani amma suka ci karo da mayakan soji, an kuma gano cewa ‘yan ta’addan sun kawo gadajen asibiti zuwa filin daga, da nufin ceto waɗanda suka jikkata—abin da ke nuna irin mummunan raunin da suka samu,” wata majiya ta tsaro ta bayyana.
Bayan kawar da ‘yan ta’addan, sojoji sun kwato makamai da alburusai masu yawa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.