Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Dakarun rundunar soji ta 6 da kuma dakarun rundunar soji na 3 karkashin Operation Whirl Stroke a jihar Taraba, sun lalata sansanonin ‘yan bindiga da dama a jihar, tare da kwato makamai da alburusai bayan.
Kakakin rundunar soji ta 6, Kyaftin Oni Olubodunde, ya ce sojojin sun gudanar da aikin ne a ranar 28 ga watan Nuwamba 2024 a ƙananan hukumomin Takum da Donga na jihar.
Ya ce harin ya mayar da hankali ne kan sansanin ƴan bindiga da maɓoyar ƴan ta’adda a kusa da babban filin Lijem, ya ƙara da cewa al’ummomin yankin sun tallafa wa sojojin in da su ka kai ga samun wannan nasarar.
Yansandan Kano sun ƙuɓutar da yarinyar da matahi ya yi garkuwa da ita ya nemi kudin fansa miliyan 3.
Sojan saman Nijeriya sun yi wa Ƴan Boko Haram fata-fata a Borno.
Masu Garkuwa sun sace mutum 30 a jihar Katsina.
A cewa Kyaftin Oni, sun gano cewa daga cikin sansanonin da ƴan ta’addan suke sun haɗar da wani sansani mai suna ‘New Gboko da Che Adekpe, wanda wani kasurgumin mai laifi mai Suna Liamdoo Douglas ya ke amfani da shi.
Acewar sa, dakarun sun ci gaba da kai sumame a ranakun 29 da 30 ga watan Nuwamba 2024 a kauyukan Kufai Ahmadu, Jam, Hingir, Ukum, da Nbaume da Kuma Sansanin ‘yan ta’adda na New Gboko da kuma Che Adekpe,inda ƙasurgumin Mai laifin da ake nema ruwa a jallo, Liamdoo Douglas Adekpe, wanda akafi sani da “Boujogh,” yake da aka dasu.
Ya ƙara da cewa, a lokacin da sojojin suka gudanar da samamen, sun fatattaki ƴan ta’addan da mugunyar wuta wanda ya tilasta musu ja da baya cikin firgici.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƴansanda sun kama mutane 7 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne a Ogun.
-
Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.
-
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
-
Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a Filato.
-
Mun mayar da yara miliyan 1.5 makaranta a Borno – Zulum.