Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Wasu rahotanni daga jamhuriyar Nijar na rundunar sojin ƙasar sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga sama da 60 da kuma ƙwato shanu 250 da ‘yan bindigar suka sace.
BBC ta rawaito cewa, sojojin sun samu wannan nasara ne a wani aiki da suka aiwatar na haɗin-gwiwa a jihar Tillabery da kuma taimaka wa manoman yankin gudanar da ayyukansu cikin tsaro a gonaki.
Bello Turji Ya Ƙarya Iƙrarin Kama Ɓaleri Da Sojojin Nijar Suka Yi.
Takunkumai: Wasu Ƴan Nijar Da Najeriya Sun Yi Zaman Dirshen A Ofishin ECOWAS da ke Nijar.
Dakarun dai na samun nasara a kan ƴanbindigar da ke addabar al’ummar ƙasar kamar yadda maƙwabciyar ƙasar Najeriya ke samun irin wannan nasara ta kamawa da kashe gomman ƴanbindigar.
Jamhuriyar Nijar dai ta jima ta na fama da ƴan bindiga da kuma masu ikirarin jihadi a sassan ƙasar, abin da ya haifar da rasa rayukan da dama, da jikkata da asarar dukiyoyi, duk da ƙoƙarin da hukumomin ƙasar ke cewa na yi na kawo ƙarshen matsalar
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.