Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar tarayyar Najeriya Aliyu Sani Madaki, ya yi martanin ga wasu ƴan majalisa na jam’iyyar NNPP da su ke son a kore shi daga muƙaminsa.
Madakin Gini ya bayyana cewa abin dariya ne a ce waɗanda ba ƴan jam’iyyar NNPP ba su yi yunƙurin cire shi daga muƙamin sa.
A wata tattaunawa da jaridar DAILY NIGERIAN, Madaki ya zargi jagoran NNPP na ƙasa, Rabi’u Kwankwaso da kitsa yunƙurin tsige shi da ga muƙamin na sa.
A cewar sa, ya za a yi waɗanda shuagabancin jam’iyya na ƙasa ya kore su samu ikon cire wani daga muƙamin sa, in da ya ƙara da cewa wani yunkuri ne na wasu da su ke rawa da bazar Kwankwaso “kuma su ke ganin cewa duk abinda ya faɗa ta zauna.”
“Waɗanda su ka rattaba hannu a takardar ba yan jam’iyyar NNPP ba ne. Kwanan nan kotu ta kori shugabancin jam’iyar bangaren Kwankwaso.
“Saboda haka wannan su na bata wa kan su lokaci ne kawai saboda kwanan nan kotu to kori shi kansa Kwankwason daga jam’iyyar. Amma ka san dole su rika rawa da bazar Kwankwaso,” in ji Madaki.
Rikicin Siyasa Na Kara Yin Zafi A Jam`Iyyar NNPP Yayin Da Kwankwasiyya Ke Rasa Jiga-Jigai.
Kano Pro-pa ta nemi Gwamnatin Kano ta tsayar da ginin wasu ajujuwan karatu.
A baya jaridar ta rawaito, wasu ƴan majalisa guda 15 cikin 18 na jam’iyyar NNPP da suke majalisar sun nemi a tsige Madaki daga muƙamin sa, sai dai babu wani dalili da aka bayyana na yin hakan, to amma wasu na ganin hakan baya rasa alaƙa da fitar Madaki daga Kwankwasiyya.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.