Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin jihar Yobe ta ƙaryata rahotanni da ake yaɗawa cewa, aƙalla sama da yara 200 cutar Sanƙarau ta kashe. A wani taron manema labarai a birnin Damaturu, kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana, ya ce cutar sanƙarau ta kashe mutum 85 tsakanin Janairu da Afrilu sakamakon ɓarkewar cutar a […]