Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Gwamnatin tarayya ta ce shugaban kasa Bola Tinubu, ya ce samar da abinci shi ne babban abin da gwamnatinsa tafi ba wa muhimmanci.
A cewar karamin ministan noma na kasar, Aliyu Abdullahi, tun bayan da aka rantsar da shugaba Tinubu a watan Mayun 2023, gwamnatinsa ta bullo da shirye-shirye da dama domin tabbatar da an wadata kasar da abinci.
Cikin wata hira da gidan talbijin na Sunrise Daily ya yi da ministan, ya ce a cikin shirye-shirye Tinubu, samar da abinci shi ne kan gaba haka kuma bunkasa aikin noma ma na cikin manyan muradun shugaban kasar saboda baya ga samar da abinci da bangaren noma zai yi zai kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.
Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Afirka ta Kudu daga Faransa.
Fadar Shugaban Najeriya Ta Karrama Shugaban Makarantar Sakandare A Jihar Zamfara.
Aliyu Abdullahi, ya ce shugaba Tinubu, ya damu matuka da matsalar karancin abincin da ake fama da ita a kasa,inda ya ce a wasu lokutan shugaba Tinubun kan sanar da su cewa babban burinsa shi ne ya kai al’ummar Najeriya matsayin da babu wanda zai kwana da yunwa.
A wannan yanayi da ake ciki, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bullo da wasu hanyoyi na saukaka rayuwa ciki har da rabon tallafin abinci ga miliyoyin ‘yan Najeriya.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.