Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba ya bayyana aniyar sa, na dai-daita jam’iyyar APC ta hanyar magance rikice-rikicen da ke addabar rassan jam’iyyar na jihohi.
Saboda haka ya umarci Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na jam’iyyar da su kafa kwamitoci don nazarin matsalolin da ke akwai, tare da kira ga shugabannin jam’iyyar a jihohi da su kasance masu hakuri da hadin kai yayin da ake kokarin samar da maslaha.
Tinubu a wurin taron jam’iyyar na kasa ya bayyana cewa “Duk da haka akwai wasu ‘yan rikice-rikice a wasu jihohi. Mu kafa kwamitoci don duba matsalolin da suka jima a jihohi, sannan mun roki shugabannin jam’iyyar a waɗannan wurare da su kwantar da hankalin su, su kuma yi aiki tare,”
Mai ba Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga, shine ya bayyana cikakken bayani game da taron a cikin wata sanarwa mai taken: “A taron APC NEC, Shugaba Tinubu ya samu kuri’ar goyon baya tare da alkawarin yin aiki tuƙuru don ci gaban Najeriya.”
A yayin taron, Tinubu ya jinjinawa Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) bisa ƙoƙarin da suke yi, tare da yin kira da a ɗauki matakan kawo karshen wasu daga cikin rikice-rikicen da ke damun jam’iyyar a jihohi.
Har ila yau, Shugaban kasa ya nanata ƙudurin sa na yin aiki tukuru don inganta rayuwar ‘yan kasa, ya na mai tabbatar da cewa tattalin arzikin Najeriya yana farfaɗo wa.
Ya ce amincewar da jam’iyyar ta nuna a kansa babban kalubale ne da ke bukatar ƙarin ƙoƙari.
Ya kuma godewa ‘yan Najeriya bisa ci gaba da amincewa da jam’iyyar APC.
Shugaban na Najeriya ya sha alwashin ci gaba da aiki tukuru tare da sauran rassan gwamnati don tabbatar da ci gaban kasa.
Ya kuma jinjinawa gwamnonin APC da shugabannin jam’iyyar bisa jajircewar su da kishin jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr Abdullahi Ganduje, ya godewa mambobin jam’iyyar bisa dagewar su duk da kalubalen da ake fuskanta, tare da tabbatar musu da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da aiwatar da alkawurran da ta ɗauka a yayin zaɓuka.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
PDP ta sake dage taron Kwamitin Zartaswar ta na Kasa (NEC) zuwa ranar 15 ga watan Mayu.
-
Mijin Sanata Matasha ya buƙaci Akpabio da ya girmama matar sa.
-
Ba zan yi musayar yawu da El-Rufai ba,-Ribadu
-
“Dubban mutane na shigowa jam’iyyar mu, ba da daɗewa ba, za mu karɓi manyan jiga-jigan NNPP da kansu”-Ganduje
-
Ƴan jam’iyyar APC sama da dubu 7 sun fice daga jam’iyyar zuwa PDP a jihar Bauchi.